An ya Arsenal za ta je Europa League a badi kuwa?

Mikel Arteta

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Arsenal ta je ta doke Crystal Palace da ci 3-1 a wasan mako na 37 a gasar Premier League da suka kara ranar Laraba a Selhust Park.

Arsenal ce ta fara cin kwallo ta hannun Nicolas Pepe saura minti 10 su je hutun rabin lokaci.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne daga hutun da suka yi, Christian Benteke ya farke wa Palace kwallon inda wasa ya koma 1-1.

Daf da za a tashi ne Gabriel Martinelli ya ci wa Arsenal na biyu, sannan Nicolas Pepe ya kara na uku, kuma na biyu da ya zura a raga a karawar.

Palace ta yi wasan ne don ban kwana da kocinta Roy Hodgson mai shekara 73, wanda ranar Talata ya sanar da zai yi ritaya a karshen kakar bana.

Hodgson ya karbi aikin horar da Palace ranar 12 ga watan Satumbar 2017, ya kuma ja ragamar wasa 161 ya ci 54 da canjaras 38 aka doke shi 69.

Da wannan sakamakon Arsenal tana mataki na tara a teburin Premier da maki 58 da tazarar maki daya tsakaninta da Everton ta takwas da kuwa Tottenham ta bakwai.

Ita kuwa Crystal Palace tana mataki na 13 a kasan teburi da maki 44, za kuma ta je Anfield ranar Lahadi domin buga wasan karshe a kakar bana.

Arsenal wadda ta buga Champions League 20 a jere da Europa League biyar za ta karbi bakuncin Brighton ranar Lahadi a Emirates.

Watakila ranar 23 ga watan Mayu ne za a tantance kungiyoyin da za su samu gurbin Champions League da wadanda za su buga Europa League a badi.

Tuni Leicester wadda ta lashe FA Cup a bana ta samu shiga gasar Europena League kai tsaye ta badi, amma tana fatan neman tikitin Champions League na kaka mai zuwa.

Tuni dai Manchester City ta lashe kofin Premier na bana, sannan Fulham da West Brom da kuma Sheffield United za su koma buga Championship a badi.