Salah na cin kwallaye duk da halin da Liverpool ke ciki a bana

Asalin hoton, Getty Images
Mohamed Salah na cin kwallaye a kakar bana duk da halin koma baya da Liverpool ta ci karo da shi a wasannin da take yi.
Dan kasar Masar wanda ya ci kwallo a ragar RB Leipzig a gasar Champions League da suka kara ranar Talata ya ci 24 jumulla a dukkakn fafatawa a 2020/21.
Liverpool ta koma ta shida a gasar Premier League ta bana, amma Salah ya zura kwallo 17 yana cikin masu takarar kyautar takalmin zinare a gasar ta Ingila.
Dan wasan ya ci uku rigis a wasan da Liverpool ta doke Leeds United 4-3 a gasar Premier League, ya kuma zura hudu a raga a karawa hudu baya a gasar.
Haka kuma Salah ya ci wa Liverpool kwallo uku a gasar FA Cup a bana.
A gasar Zakarun Turai kuwa dan wasan tawagar Masar ya ci hudu a karawa takwas a Champions League a bana.
Wannan ce kaka ta hudu da Salah ke taka leda a Liverpool ya kuma kara kwazo kan yawan kwallayen da yake ci a kowacce kakar tamaula.
Watakila dan wasan ya yi bajintar da ya yi a 2018/19 ko ya haura haka, wanda ya ci kwallo 27 jumulla a dukkan fafatawa da 22 a gasar Premier League.
A lokacin ya lashe kyautar takalmin zinare tare da Sadio Mane da kuma dan kwallon Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang.









