Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Valverde, Rabiot, Alaba, Upamecano, Haaland, Sancho, Sturridge
Manchester United na sanya ido kan dan wasanReal Madrid da Uruguay Federico Valverde, mai shekara 22. (Sun)
Everton za ta sake sabon yunkurin daukar dan wasan Juventus da Faransa Adrien Rabiot, mai shekara 25, a bazarar nan. (Mail)
Dan wasan Marseille da Croatia Duje Caleta-Car, mai shekara 24, ya ce ya yi watsi da tayin tafiya Liverpool a watan Janairu. (Goal)
Dan wasan Austria David Alaba, mai shekara 28, yana son tafiya Real Madrid da zarar ya bar Bayern Munich a karshen kakar wasa ta bana kuma tuni ya soma koyon harshen Sifaniya - amma tafiyarsa Bernabeu za ta dogara ne da makomar dan wasan Real dan kasar Sifaniya Sergio Ramos. (Mirror)
Har yanzu Alaba shi ne dan wasan da ke sahun gaba a cikin wadanda Real take so n dauka domin ya maye gurbin Ramos, mai shekara 34, kodayake dan wasan RB Leipzig da ke shirin tafiya Bayern Munich Dayot Upamecano, mai shekara 22, ya kasance zabinsu kafin yanzu. (AS - in Spanish)
Manchester United ta kusa kammala sayen Upamecano a kan £1.9m a shekarar 2015, a cewar mai bai wa dan wasan shawara. (Mirror)
Kokar koci dan kasar Portugal Jose Mourinho zai sa Tottenham ta y asarar euro 40m (£34.8m). (A Bola - in Portuguese)
Kocin RB Leipzig Julian Nagelsmann da takwaransa na Leicester Brendan Rodgers na cikin wadanda mai yiwuwa za su maye gurbin Mourinho a Tottenham. (Mail)
A baya shugaban Spurs Daniel Levyya yi yunkurin daukar tsohon kocin Liverpool da Celtic Rodgers kuma mai yiwuwa ya sake gwada yin hakan idan Mourinho ya sauka daga kan mukamin. (Eurosport)
Dan wasan Demarai Gray, mai shekara 24, ya ce ba a sabunta kwangilarsa aLeicester ba kafin ya tafi Bayer Leverkusen a watan Janairu. (Sky Sports)
Mai yiwuwa Manchester United ta mayar da hankali wajen daukar sabon dan wasan tsakiya ko kuma dan wasan Borussia Dortmund dan kasarNorway Erling Braut Haaland, mai shekara 20, a kan dan wasan Dortmund dan kasar Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, bayan da ta tsawaita kwangilar dan wasan Ingila mai shekaera 19, Mason Greenwood. (Express)
Manchester United ta shirya biyan euro 70m (£60m) domin ta buge Real Madrid da Paris St-Germain a fafatawar da suke yi wajen sayen dan wasan Sevilla dan kasar Faransa mai shekara 22 Jules Kounde. (TeamTalk)
Real Madrid ta bi sahun kungiyoyin da ke son daukar dan wasan Braga dan kasar Portugal David Carmo. Liverpool ta yi yunkurin daukar dan wasan mai shekara 21 a watan Janairu amma tattaunawa kan hakan ta wargaje. (AS - in Spanish)