Transfer rumours: Konsa, Mbappe, Gundogan, Lingard, Aarons, Medina

An wallafa

Liverpool na duba yiwuwar dauko Ezri Konsa, dan wasan baya na Aston Villa mai shekara 23, nan da karshen wannan kakar wasan. (Athletic - subscription required)

Liverpool, da Manchester United, da Manchester City da kuma Tottenham na sha'awar daukan Mathew Hoppe, dan wasan Schalke mai shekara 19 domin ya buga mu su. Lamarin ya zama na mai rabo ka samu. (90min)

Dan wasan gaba na Paris St-Germain da Faransa, Kylian Mbappe ya gaya wa kungiyar tasa cewa zai yi zamansa tare da ita har zuwa 2022, lokacin da kwantiraginsa ta yanzu za ta kawo karshe. (Sport - in Spanish)

Dan wasan Manchester City da Jamus Ilkay Gundogan mai shekara 30, ya fara tunanin ritaya daga buga kwallo, inda ya sanar cewa yana son zama koci ne bayan ya bar kwallon kafa. (Goal)

An fara gwajin dawo da 'yan kallo a wasannin da za a buga na gasar cin kofin kalubale ko FA Cuo da wasan karshe na gasar Carabao. (Times - subscription required)

Crystal Palace ta bayyana kocin Swansea Steve Cooper a matsayin mutumin da ka iya maye gurbin kocinta na yanz Roy Hodgson. (Sun)

Chelsea ce kungiya daya tilo daga Ingila da ta yi wa David Alaba, dan wasan baya mai shekara 28 na Bayern Munich da Austria tayin kwantiragi. (90min)

Norwich ta sanar da Bayern Munich sai ta yi aman fam miliyan 30 zuwa 35m idan su na son raba ta da Max Arons, dan wasan baya dan Ingila maishekara 21. (Sky Sports)

Harry Kane, dan wasan gaba na Ingila da Tottenham, cikin sirri ya gaya wa abokansa cewa kocin Tottenham Jose Mourinho na goyon bayansa. (Football Insider)