Mbappe ya ragargaji ragar Barcelona a Nou Camp

An wallafa

Paris St Germain ta casa Barcelona da ci 4-1 a gasar Champions League wasan farko karawar zagaye na biyu da suka fafata ranar Talata a Nou Camp.

Lionel Messi ne ya fara zura kwallo a ragar PSG wadda ta buga wasan karshe a bara a gasar da Bayern Munich ta doke ta 1-0.

Bayan da Messi ya fara cin kwallo a minti na 27 da fara tamaula, PSG ta kara sa matsi, inda ta farke ta hannun Kylian Mbappe, sannan ya kara na biyu.

Dan kwallon Everton, Moise Kean da ke buga wasa aro ne ya kara ci wa PSG kwallo, kuma na uku a fafatawar da ya bai wa kungiyar da ke buga Ligue 1 kwarin gwiwa.

Barcelona ta yi ta kai kora don ta zare kwallayen da aka zura mata, amma hakan bai yiwuba, sai PSG ta kai wata kora kuma Mbappe ya ci na hudu kuma na uku a wasan.

Barcelona za ta ziyarci Faransa ranar 20 ga watan Maris domin buga wasa na biyu da ake sa ran watakila Neymar ya warke ya kuma fuskanci tsohuwar kungiyarsa.

Mai tsaron bayan ya koma yin atisaye tun ranar Alhamis, kuma ya samu kuzarin da zai iya buga wasan da Barcelona za ta karbi bakuncin PSG din.

Ronald Araujo bai murmure da wuri ba domin buga wasan, amma Martin Braithwaite ya samu koshin lafiyar da zai iya buga fafatawar.

'Yan Barcelona 21 suka fuskanci PSG:

Masu tsaron raga: Marc-Andre ter Stegen da Neto da kuma Inaki Pena.

Masu tsaron baya: Sergino Dest da Oscar Mingueza da Gerard Pique da Clement Lenglet da Samuel Umtiti da Jordi Alba da kuma Junior Firpo.

Masu buga tsakiya: Sergio Busquets da Frenkie de Jong da Pedri da Riqui Puig da Miralem Pjanic da kuma Matheus Fernandes.

Masu cin kwallo: Lionel Messi da Antoine Griezmann da Ousmane Dembele da Francisco Trincao da kuma Martin Braithwaite.