Premier League: Man City ta ragargaje Liverpool har gida

An wallafa

Manyan kusukure biyu da golan Liverpool Alisson Becker ya yi sun taimaka wa Manchester City ɗura ƙwallo har huɗu a ragar zakarun na Premier League a wasan mako na 23.

Kazalika, ƙungiiyar ta Guardiola ta bayar da tazarar maki biyar a saman teburin gasar.

Gündogan ne ya fara zira ƙwallo a minti na 49 bayan ya zubar da finareti kafin a tafi hutun rabin lokaci sakamakon ƙetar da Fabinho ya yi wa Sterling.

Mohamed Salah ya farke wa Liverpool a minti na 63 daga bugun finareti kafin daga bisani Sterling da Foden su ƙara ta uku da ta huɗu.

Yanzu haka akwai tazarar maki 10 tsakanin City a saman teburi da kuma Liverpool a mataki na huɗu bayan wasan da aka buga a Anfield.