Champions League: Man City za ta kara da Borussia a Hungary

An wallafa

Manchester City za ta buga wasan zagaye na biyu a Champions League da Borussia Monchengladbach a Hungary.

Hakan ya biyo bayan da gwamnatin Jamus ba ta amince da aka buga wasan a kasarta ba, saboda gudun yada cutar korona.

Jamus ta hana a shiga kasarta musamman ta jirgin sama ga kasashen da cutar korona ke kara yi wa ta'adi ciki har da Burtaniya.

Borussia za ta karbi bakuncin City a wasan farko a matakin gidanta ranar 24 ga watan Fabrairu a Fuskas Aarsena da ke Budapest a fafatawar kungiyoyi 16 da suka rage a gasar ta bana.

Shi ma wasan da Liverpool ya kamata ta fafata da RB Leipzig a Jamus za a yi shi a Hungary.

Kungiyoyin biyu za su kara ranar 16 ga watan Fabrairu, sannan Liverpool ta karbi bakuncin wasa na biyu.

Manchester City za ta yi wa Borussia masauki a fafatawa ta biyu ranar 16 ga watan Maris.