Watakila Bayern Munich ta lashe kofi shida a kaka daya

Asalin hoton, EPA
Ranar Alhamis Bayern Munich za ta kara da Tigres ta Mexico a wasan karshe a gasar cin kofin duniya ta zakarun nahiyoyin duniya wato Club World Cup da ake yi a Qatar.
Idan Bayern ta yi nasarar lashe kofin za ta zama ta biyu bayan Barcelona da ta lashe kofi shida a gasar gida da ta duniya a jere a kakar tamaula.
Kawo yanzu kungiyar ta Jamus ta ci kofin Champions League da Super Cup da German Super Cup da Bundesliga da kuma German Cup.
Ana yin wasannin Club World Cup don yin gwaji ga kasar da za ta karbi bakuncin gasar kofin duniya wato Qatar a 2022.
Kuma tun cikin shekarar 2020 ya kamata a buga wasannin, amma bullar cutar korona ta sa aka dage fafatawar zuwa 2021.
Ranar Litinin Bayern ta kai wasan karshe, bayan da ta doke Al Ahly ta Masar daga nahiyar Afirka.
Sai dai kuma Bayern za ta yi wasan karshe ba tare da 'yan was anta Leon Goretkza da kuma Javi Martinez.
Shi Martinez yana Jamus ya killace kansa, bayan da ya kamu da cutar korona.











