Me ya sa 'yan wasan Real Madrid ke yawan rauni?

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta kara da Getafe a kwantan wasan makon farko a gasar La Liga da za su fafata ranar Talata.
Sai dai kuma Real na fuskantar kalubale, bayan da 'yan wasanta da dama ke jinya a kakar tamaula ta bana.
Eder Militao da kuma Alvaro Odriozola su ne na baya-bayan nan da suka shiga jerin masu jinya a kungiyar.
'Yan wasan da ke jinya kawo yanzu sun hada da Sergio Ramos da Dani Carvajal da Lucas Vazquez da Eder Militao da Fede Valverde da Eden Hazard da kuma Rodrygo.
Haka kuma wani dan wasan Alvaro Odriozola ya yi rauni, yayin da Toni Kroos ke hutun hukunci kan kati biyar aka ba shi, saboda haka ba zai buga wasan Getafe ba.
Real ta damu da raunin da 'yan wasanta ke yi da ya kai sau 38, ko da yake ana alakanta wasannin da ake yi kusa da kusa, sakamakon cutar korona da ta haddasa.
Haka kuma Real Madrid ba ta sayi dan kwallo ba a kakar bana, saboda haka 'yan wasa ba sa hutu yadda ya kamata, har ta kai hutu shi ne idan ka yi rauni.
A kalla dai 'yan kwallon Real Madrid 20 ne suka yi rauni ko dai a karon farko wasu ma sau bibiyu a kakar 2020/21.
Sai dai abin da ya kamata kungiyar ta bincika shi ne ko 'yan kwallon na yin rauni ne sakamakon yadda ake jinyar mutum ya koma tamaula da wuri?
Ko kuma rashin samun motsa jiki da ya dace da zai yi daidai da wasan da dan kwallo zai fuskanta kafin buga tamaula?
Wasu lokacin 'yan kwallo na sawa kansu matsi ganin sun sa kwazon da zai kai kungiyar wani mataki da hakan ya sa mutum ya yi rauni.
Real Madrid ita ce da kofin La Liga na bara, sai dai tana ta uku a teburi, bayan da Atletico ke jan ragama sai kuma Barcelona ta biyu.
Idan har Real ba ta kara sa kaimi ba a bana za ta iya karkare kakar ba tare da lashe kofi ba, domin ta rasa Spanish Super Cup da Copa del Rel kawo yanzu.
Yanzu dai kofin da Real ke hari shi ne na Champions League da ta kai zagaye na biyu da za ta fafata da Atalanta cikin watan Fabrairu.
Haka kuma ana fafatawa da ita a La Liga, koda yake Atletico ta bata tazarar maki bakwai, bayan da aka buga wasannin mako na 22.









