'Yan wasan Real Madrid da za su fafata da Getafe

Real Madrid

Asalin hoton, Real Madrid Twitter

An wallafa

Real Madrid za ta ziyarci Getafe domin buga gasar La Liga ranar Talata.Tuni kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasan da za su buga masa wasan.

Cikin 'yan wasan da za su murza leda har da Isco wanda ya yi atisaye tare da 'yan wasan a safiyar Litinin.Real na fama da 'yan wasa da ke jinya da suka hada da Sergio Ramos da Dani Carvajal da Lucas Vazquez da Eder Militao da Fede Valverde da Eden Hazard da kuma Rodrygo.

Haka kuma wani dan wasan Alvaro Odriozola ya yi rauni, yayin da Toni Kroos ke hutunhukuci kan kati biyar aka ba shi.

Hakan ne ya sa Zidane ya gayyato matasan Real Madrid biyar da suka cika 19 da za su fuskanci Getafe ranar ta Talata.Matasan da Zidane ya gayyato sun hada da Victor Chust da Miguel Gutierrez da Marvin Park da Sergio Arribas da kuma Antonio Blanco.'Yan wasan Real Madrid da za su fuskanci Getafe:Masu tsaron raga: Thibaut Courtois da Andriy Lunin da Diego Altube.Masu tsaron baya: Raphael Varane da Nacho da Marcelo da Ferland Mendy da Victor Chust da kuma Miguel Gutierrez.Masu buga tsakiya: Luka Modric da Casemiro da Isco da Marvin Park da Sergio Arribas da kuma Antonio Blanco.Masu cin kwallaye: Karim Benzema da Marco Asensio da Vinicius Jr da kuma Mariano Diaz.