Shin Barcelona ta koma kan ganiyarta ne?

An wallafa

Ranar Lahadi Barcelona ta doke Athletic Bilbao da ci 2-1 a wasan mako 21 a gasar La Liga da suka fafata a Camp Nou.

Lionel Messi ne ya fara ci wa Barcelona kwallo kuma na 650 da ya ci a kungiyar sannan na 49 da ya zura a raga a bugun tazara.

Wannan sakamakon ya kai Barcelona ta koma ta biyu a kan teburin La Liga da maki 40 iri daya da wanda Real Madrid ta uku a teburi take da shi.

Kuma Barcelona ta yi wasa 10 a jere a gasar La Liga ba ta tare da an doke ta ba, wadda ta ci karawa takwas da canjaras biyu.

Kocin Barcelona na yin wannan kokarin ba tare da 'yan wasa da suka hada da Gerard Pique da Ansu Fati da Philippe Coutinho da kuma Sergi Roberto da ke jinya.

'Yan kwallon Barcelona Oscar Mingueza na taka rawar gani daga baya haka ma Antoine Griezmann da kuma Frenkie de Jong da ke cin kwallaye sannan Ousmane Dembele da ya kara tsayawa da kafafunsa.

Kuma salon da Barcelona ta koma na 4-3-3 ya ba ta damar taka leda mai kayatarwa da kai hare-hare da dama a lokacin da take wasanninta.

Barcelona tana ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki 10 tsakaninta da Atletico Madrid ta daya tana kuma cikin gasar Copa del Rey, sannan ta kai zagaye na biyu a Champions League a bana.

Yanzu da aka fada zagaye na biyu a gasar La Liga ga kuma wasannin bana sun fara shiga gangara, kuma Barcelona na saka kwazo kawo yanzu.

Abin tambaya ko za ta kai labari nan da karshen kakar bana?