Barcelona 2-1 Athletic Bilbao: Lionel Messi ya ci kwallaye 650 a zamansa a Barca

An wallafa

Lionel Messi sya zura kwallo ta 650 a wasan da ya buga wa Barcelona a karawar da suka yi da Athletic Bilbao inda yanzu suke na biyu a teburin La Liga.

'Yan wasan Athletic biyar ne suka yi katanga, daya kuma yana tsaye a bayanta yayin da daya ya tsaya a kan layi amma sai da Messi ya cilla kwallon cikin ragar kungiyar.

Athletic ta farke kwallonta ta hannun Jordi Alba.

Sai dai Antoine Griezmann ya zura kwallon da ta ba su nasara bayan Oscar Mingueza ya mika masa ita.

Barcelona ta sha gaban Real Madrid a yawan kwallaye, sai ai dukkansu suna bayan Atletico Madrid da maki 10- kuma za ta fafata da su bayan da ta doke Cadiz a ranar Lahadi.

Da alama 'yan wasan Ronald Koeman sun kawo karshen kamfar zura kwallaye da suka yi fama da ita a farkon kakar wasan bana inda suka yi nasara a wasa takwas sannan suka yi canjaras a wasanni biyu a wasanni 10 da suka kara a gasar La Liga.

Barcelona ta rufe ranar ta Lahadi ne fiye da yadda ta soma ta, yayin da ta yi watsi da rahotannin da ke cewa ta tsegunta wa jaridar El Mundo kwantaragi Messi.

Kungiyar ta Sifaniya tana sirin maka jaridar a kotu saboda wallafa kwangilar Messi wacce ta kai ta £492m.