Arsenal ta kusan kammala daukar Martin Odegard

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na dab da kammala daukar Martin Odegard daga Real Madrid a cikin makon nan.
Mai shekara 22 dan kasar Norway bai samu lokacin buga wa Real wasanni sosai ba a karkashin koci Zinedine Zidane a kakar bana.
Kungiyar Real Sociedad da Ajax na son daukar Odegard wanda ya buga musu wasannin aro a baya.
Tuni Arsenal ta cimma yarjejeniya da Real Madrid na daukar dan kwallon da take sa ran kila ya buga mata wasa da Manchester United ranar Asabar.
Masannin harkokin wasanni Guillem Balague ya ce Real Madrid ta zabi dan kwallon ya je buga gasar Premier League maimakon Real Sociedad.
Zai kuma je Emirates bayan da Mesut Ozil ya koma Fenerbahce da buga gasar Turkiya.
Odegard ya koma Real Madrid daga Stromgodset a Janairun 2015 ya kuma buga wa Real Madrid wasa tara a kakar bana.
Real Madrid tana ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki bakwai tsakaninta da Atletico Madrid mai kwantan wasa daya.
Arsenal tana ta 11 a teburin Premier League da maki 29, bayan buga karawa 19.









