Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Ings, Lukaku, Barella, Medina, Lingard, Alli
Tottenham na shirin dauko Danny Ings, dan wasan gaba na Southampton da Ingila mai shekara 28 nan da karshen kakar wasan nan. (Eurosport)
Kocin Southampton Ralph Hasenhuttl ya ce kungiyar ba za ta iya kara albashin manyan 'yan wasa kamar Ings ba saboda halin matsin tattalin arziki da ta ke fuskanta. (Mirror)
Ings dai na fatan samun kungiyar da zai buga gasar Zakarun Turai da ita, shi yasa ya ke ja da baya da tsawaita zamansa a Southampton. (Telegraph)
Dan wasan gaba na Inter Milan da Belgium, Romelu Lukaku, mai shekara 27 ya ce ba shi da sha'awar komawa Manchester City. (Express)
Liverpool da Tottenham na rige-rigen daukan Nicolo Barella, dan wasan Inter da Italiya mai shekara 23. (Calciomercato)
Liverpool da Barcelona ba su cire ran dauko David Alaba, dan wasan Bayern Munich da Austria mai shekara 28 ba, duk da cewa Real Madrid na daf da yin gaba da shi. (Sport1)
Manchester United na shirin yin tayin fam miliyan 11 ga Facundo Medina, dan wasan Lens da Argentina mai shekara 21. (La Voix du Nord - in French)
Nice ta janye bukatar da ta ke da ita ta daukan aron Jesse Lingard, dan wasan Manchester United da Ingila mai shekara 28. (Sky Sports)
Dan wasanTottenham da Ingila, Dele Alli mai shekara 24 na da karfin gwuiwar komawa Paris St-Germain a wannan watan na janairu a matsayin dan wasa na aro. (Sun)
Amma fatan na Dele Alli ya danganta ne kan bukatun da Spurs za su dora wa PSG. (Goal)
An sanar da Arsenal cewa Emi Buendia, dan wasan Norwich City da Argentina mai shekara 24 ba zai bar kungiyarsa ba a wannan kasuwar 'yan kwallon da ke ci a yanzu. (Independent)
Manchester City na da wani shirin dawo da Douglas Luiz, dan wasan tsakiya na Aston Villa da Brazil kan fam miliyan 27.5, amma ba a ganin Pep Guardiola zai bukaci dan wasan mai shekara 22. (Birmingham Mail)