An ya Neymar zai so ya sake komawa Barcelona kuwa?

An wallafa

Ranar 3 ga watan Agustan 2017 Neymar ya koma Paris St Germain da taka leda daga Barcelona a matakin wanda aka saya mafi tsada a duniya.

Wasu rahotanni na cewa daya daga dalilan da suka sa ya bar Spaniya shi ne yana son yin suna na kashin kansa, bayan da Lionel Messi ya hana shi haskakawa a fanni kwallon kafa.

Neymar ya taka rawar gani a Barcelona, amma duk wani ƙwazon da ya saka, sai an fara hangen kyaftin Lionel Messi kafin dan kwallon Brazil din.

Sai dai bayan da Neymar ya koma Paris St Germain da taka leda daga baya ya hangi kamar ya yi kuskuren komawa Faransa da taka leda.

Daga nan ya fara samun matsala a wasannin da jawao cece-kuce da ta kai magoya baya suka dunga kiraye-kirayen gara ya san inda dare ya yi masa.

Ba inda Neymar ya hanga sai Barcelona wadda yake gani zai cika burinsa na zama fitatcen dan wasa a duniya ko kuma ya gaji Messi a kungiyar ta Spaniya.

Paris St Germain daya ce daga kungiyar Turai da ta tsara yadda za ta zama fitatciya a fagen tamaula a nahiyar dama duniya.

Sai dai bullar cutar korona ta damalmala komai, inda kungiyoyi suka shiga kaka ni kayi, tattalin arzikinsu ya girgiza har da Barcelona.

Kungiyar ta Camp Nou ta kasa lashe kowanne irin kofi a bara, kuma kyaftin dinta Lionel Messi ya bukaci barin Spaniya da taka leda, sannan shugaba Joseph Mario Bartemeo ya yi murabus.

Wasu labaran wasanni da za ku so

Abubuwa da dama sun faru a Barcelona da ya jawo take kasa taka rawar gani a bana duk da daukar sabon koci Ronald Koeman, kungiyar tana ta uku a teburin La Liga za ta buga Spanish Super Cup da Real Sociedad ranar Laraba.

Neymar ya kwantar da hankalinsa a wasannin da yake buga wa a Paris St Germain, bayan da Kylian Mbappe ya zama abokinsa suke kuma buga tamaula ta ban sha'awa.

Wasu rahotanni na cewar daraktan wasanni na PSG, Leonardo shi ne ya rarrashi Neymar ya kuma fayyace masa tsare-tsaren da kungiyar ke yi na ganin ta zama zakara a Turai da duniya.

A farkon shekarar 2021 PSG ta sallami koci Thomas Tuchel ta dauki Mauricio Pochettiono, kuma burun kungiyar shi ne lashe Champions League, wanda ta kai wasan karshe a bara, Bayern Munich ta doke ta.

Bisa alamu dai Neymar ya hakura zai ci gaba da taka leada a Faransa, kuma kawo yanzu ya buga wa PSG wasa 12 a bana ya kuma zura kwallo tara a raga.

Paris St Germain tana mataki na biyu a teburin Ligue 1 da tazarar maki daya tsakaninta da Lyon, bayan buga wasannin mako na 19 a gasar ta Faransa.