Atletico ta kara bayar da tazara tsakaninta da Real a La Liga

An wallafa

Atletico Madrid ta bai wa Real Madrid tazarar maki hudu a gasar La Liga, bayan da ta doke Sevilla 2-0 a kwantan wasan da ta buga ranar Talata.

Kungiyar da Diego Simeone ke jan ragama ta fara cin kwallo ta hannun Angel Correa, bayan da Kieran Trippier ya bashi fasin.

Karon farko da dan kwallon tawagar Ingila Tripper ya buga wa Atletico Madrid, bayan da hukumar kwallon kafa ta duniya ta dakatar da hukuncin hana shi taka leda mako 10, bayan da ya karya dokar yin caca.

Fifa ta dakatar da hukuncin ne bayan da Atletico ta daukaka kara kan laifin da Trippier ya aikata a lokacin da zai koma Spaniya da taka leda daga Tottenham.

Atletico ta kara kwallo na biyu a minti na 76 da hakan ya bai wa kungiyar maki ukun da take bukata.

Wannan ne karon farko da aka doke Sevilla a wasa 10 da ta buga a La Liga, bayan da take ta shida a saman teburi.

Wasu labaran wasanni da za ku so

Kawo yanzu Atletico wadda take da kwantan wasa biyu ta hada maki 41 daga karawa 16 a La Liga da tazarar maki hudu tsakaninta da Real Madrid wadda take ta biyu.

Real Madrid za ta kara da Athletic Bilbao a wasan daf da karshe a Spanish Super Cup, kwana shida tsakani ta fafata da Alcoyano a Copa del Rey.

Ranar Asabar 23 ga watan Janairu, Real Madrid za ta ziyarci Alaves domin buga gasar La Liga.

Ita kuwa Atletico za ta ziyarci Eibar ranar 21 ga watan Janairu a wasan La Liga, bayan da tuni aka fitar da ita a Copa del Rey, ba ta buga Spanish Super Cup.