Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kano Pillars za ta kara da Plateau United a gasar Firimiyar Najeriya
Kungiyar Kano Pillars za ta fafata da ta Plateau United a wasan mako na hudu a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria ranar Laraba.
Pillars, wadda ke buga wasanninta a jihar Kaduna, ta ci fafatawa daya da canjaras biyu mai maki biyar za ta kece raini da Plateau wadda ke da maki hudu.
Rivers United wadda ke jan ragamar teburi da maki tara za ta ziyarci Wikki mai maki daya jal.
Wasu wasannin hamayya da zai yi zafi sun hada da na Adamawa United da Katsina United da wanda Heartland za ta karbi bakuncin Enyimba International, koda yake har yanzu Heartland ba ta da maki.
Wasannin mako na hudu da za a kara ranar Laraba:
Adamawa United da Nasarawa United
Kano Pillars da Plateau United
Heartland da Enyimba International
Warri Wolves da Katsina United
Sunshine Stars da Lobi Stars
Dakkada da Mountain Of Fire And Miracles
Enugu Rangers International da Ifeanyi Ubah F
Abia Warriors da Jigawa Golden Stars
Kada City da Akwa United
Wikki Tourists da Rivers United