Dan gidan Thuram ya yi dana sanin tofa wa Posch yawu a fuska

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Borussia Monchengladbach, Marcus Thuram ya nemi afuwa, bayan da aka yi masa jan kati, sakamakon tofa wa Stefan Posch yawu a fuska.
An bai wa dan kwallon tawagar Faransa jan kati kai tsaye a minti na 79 ranar Asabar a karawar da aka doke su 2-1, bayan VAR ta fayyace laifin da ya aikatawa dan kasar Ausria.
Borussia Dortmund ta sanar cewar za ta ci tarar Thuram da kuma dakatar da shi wasu wasannin.
Wannan ne karon farko da aka bai wa dan gidan Lilium Thuram jan kati a Borussia Monchengladbach a kaka biyu da yake taka leda a gasar Bundesliga ta Jamus.
Marcus ya nemi afuwa ga dan wasan Hoffenheim, Stefan Posch da abokan taka ledarsa da koci da magoya bayan Gladbach cewar hakan ba zai sake faruwa ba.
Kungiyar ta Jamus ta ce za ta ci tarar Marcus daidai da albashinsa na wata daya, domin wannan ne karon farko da ya aikata laifin.
Za kuma ta bayar da kudin tarar dan wasan ga kungiyoyin agaji, domin taimakawa masu karamin karfi su amfana.
Gladbach wadda za ta kara da Manchester City a wasan zagaye na biyu a Champions League tana ta takwas a kan teburin Bundesliga.
Kungiyar ba ta ci wasa ko daya ba daga shida da ta buga a dukkan karawa a kwanan nan ba, ita kuwa Hoffenheim ta yi sama zuwa ta 11 a teburin gasar Jamus.











