Kasuwar cinikin 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Rice, Origi, Rojo, Ibanez, Haaland

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United tana iya yunkurin daukar dan wasan West Ham Declan Rice, ko da yake ana tunani dan wasan na Ingila mai shekara 21 ya fi son tafiya Chelsea idan ya bar Hammers. (Express)
Wolves na sanya ido kan dan wasan Liverpool da Belgium Divock Origi, mai shekara 25, wanda za a iya bari ya kama gabansa a watan Janairu. (Mail)
Manchester United na kokarin ganin ta bayar da aron Marcos Rojo a watan Janairu, a yayin da Newcastle ke son daukar dan wasan na kasar Argentina, mai shekara 30. (The Athletic - subscription required)
Liverpool ta sanya dan wasan Roma Roger Ibanez a jerin 'yan wasan da take son dauka domin maye gurbin dan wasanta da ke jinya dan kasar Netherlands Virgil van Dijk, mai shekara 29, kuma za ta iya kashe £30m don dauko dan kasar ta Brazil. (AS Roma Live, via Team Talk)
Dan takarar shugabancin Barcelona Victor Font ya ce ba zai maimaita kuskuren 'yan takarar da suka gabata ba ta hanyar fitowa fili ya yi alkawarin musayar 'yan kwallo, a yayin da ake alakanta shi da dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Norway Erling Haaland, mai shekara 20, amma yana fatan rarrashin dan wasan Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, domin ya sabunta kwangilarsa. (Goal)
Dan wasan tsakiyar Hungary Dominik Szoboszlai, mai shekara 20, wanda Arsenal ke son dauka, ya kammala tafiya RB Leipzig daga Red Bull Salzburg, kuma a watan Janairu zai sanya hannu kan kwangilar shekara hudu da rabi. (Mirror)
Bayanai na nuna cewa Arsenal na shirin kammala kulla yarjejeniya da dan wasan Hertha Berlin Omar Rekik bayan dan wasan mai shekara 18 ya isa London ranar Alhamis. (Metro)
Napoli za ta bukaci a biya ta akalla £14m idan ana so ta sayar da dan kasar Poland Arkadiusz Milik a watan Janairu a yayin da Juventus, Everton da Atletico Madrid suke son dan wasan mai shekara 26. (Goal)
Celtic na tattaunawa da golan Northern Ireland Conor Hazard, mai shekara 22, domin sabunta kwangilarsa ta dogon lokaci. (Football Insider)
Manchester United na tattaunawa da dan wasan Celta Vigo dan shekara 16 Stefan Bajcetic domin ya tafi Old Trafford. (La Voz de Galicia, via Sport Witness)












