Supercopa Espana: Barca da Atletico, Real da Athletic Club

Supercopa de Espana

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

An raba jadawalin Supercopa Espana da za a fafata tsakanin Real Sociedad da Barcelona da Real Madrid da kuma Athletic Club a cikin watan Janairun 2021..

Kofin na 2020/21 da za a buga shi ne na 35 da ake yi tsakanin fitattun kungiyoyin Spaniya da suka yi fice a kakar tamaula.

Za a yi wasannin ne kamar haka: Real Madrid wadda ta lashe kofin La Liga a bara da Barcelona wadda ta yi ta biyu a La Ligar da aka kammala

Athletic Club wadda ta kai wasan karshe a Cope del Rey 2019/20 da kuma Real Sociedad wadda ta kai karawar karshe a Copa del Rey a 2019/20.

A jadawalin Real Sociedad za ta fafata da Barcelona da wasan da za a buga tsakanin Real Madrid da Athletic Club.

Za a fara karawar tsakanin 13 da 14 ga watan Janairu a kuma buga wasan karshe ranar 17 ga watan Janairun 2021.

Za kuma a yi amfani da filin wasa uku don fitar da gwana, inda karawa tsakanin Real Sociedad da Barcelona za a yi a Nuevo Arcangel a Cordoba.

Filin wasa na La Rosaleda a Malaga zai karbi karawa tsakanin Real Madrid da Athletic Club.

Estadio de La Cartuja da ke Seville ne zai karbi bakuncin wasan karshe.

A wasan mata kuwa a Supercopa Espana za a yi ne tsakanin Levante da Logrono da fafatawa tsakanin Atletico Madrid da Barcelona.

Tun farko an tsara buga wasannin a Saudi Arabia a badi kamar yadda aka yi a bara, sai dai gudun yada cutar korona ta sa za a yi gumurzun a Spaniya.