Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a tarihin Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Cristiano Ronaldo da Lionel Messi ne ke kan gaba a matakin wadanda suka ci kwallo fiye da 100 a gasar Zakarun Turai.
Ranar Laraba Ronaldo ya ci kwallo na 135 a gasar Zakarun Turai a wasan da Juventus ta doke Dynamo Kiev da ci 3-0.
Kyaftin din Portugal shi ne ya zura na biyu a raga a fafatawar, kuma na 750 da ya ci tun bayan da ya fara sana'ar kwallon kafa.
Lionel Messi bai buga wasan da Barcelona ta yi nasara a gidan Ferencvarosi ta Hungary da ci 3-0 ranar Laraba ba.
Kawo yanzu Ronado ya ci kwallo 135 a gasar Champions Legue, shi kuwa Messi yana da 121 a raga, kuma su kadai ne suka ci fiye da 100 kawo yanzu.
Kuma lissafin ya hada da dukkan wasannin gasar cin kofin zakarun Turai tun lokacin da aka fara fafatawar.
Ga jerin 'yan wasan da ke kan gaba a cin kwallaye a gasar Champions League da kungiyoyin da suka buga wa kwallo:
- Cristiano Ronaldo (Sporting CP, Manchester United, Real Madrid, Juventus) 135
- Lionel Messi ( Barcelona) 121
- Robert Lewandowski (Lech Poznań, Borussia Dortmund, Bayern München) 78
- Raúl González (Real Madrid, Schalke) 77
- Filippo Inzaghi (Parma, Juventus, AC Milan) 70
- Karim Benzema (Lyon, Real Madrid) 68
- Andriy Shevchenko (Dynamo Kyiv, AC Milan, Chelsea) 67
- Sergio Agüero (Atlético Madrid, Manchester City) 62
- Ruud van Nistelrooy (Heerenveen, PSV Eindhoven, Manchester United, Real Madrid, Hamburg) 62
- Gerd Müller ( Bayern München) 62
- Thierry Henry (Monaco, Juventus, Arsenal, Barcelona) 59
- Henrik Larsson (Feyenoord, Celtic, Barcelona, Manchester United, Helsingborg) 59
- Zlatan Ibrahimović (Ajax, Juventus, Internazionale Milano, Barcelona, AC Milan, Paris Saint-Germain, Manchester United) 57
- Eusébio ( Benfica) 56
- Klaas-Jan Huntelaar (Heerenveen, Ajax, AC Milan, Schalke) 55
- Alessandro Del Piero (Juventus) 54
- Didier Drogba (Marseille, Chelsea, Galatasaray) 50
- Alfredo Di Stéfano (Real Madrid) 50




