Barcelona za ta ziyarci Ferencvaros da 'yan kwallo 20 a Champions League

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ronald Koeman zai ziyarci Hungary da 'yan wasa 20, domin karawa da Ferencvaros a Gasar Champions League ranar Laraba.

Barcelona wadda tuni ta kai zagaye na biyu a gasar bana, za ta kara da kungiyar Hungary a wasa na biyar-biyar a cikin rukunin na bakwai.

Barcelona ce ta daya da maki 12 a rukuni na bakwai, sai Juventus ta biyu da maki tara, yayin da Dynamo Kiev da kuma Ferencvaros kowacce keda maki dai-dai.

A wasan farko da suka fafata a cikin rukunin, Barca ce ta yi nasara a kan Ferencvaros da ci 5-1 a Camp Nou.

Haka kuma ranar Laraba Dynamo Kiev za ta ziyarci Juventus, kuma Juventus ce ta doke Dynamo Kiev 2-0 a wasan farko a Ukraine.

Tuni dai kocin Barcelona, Ronald Koeman ya bayyana 'yan kwallo 20 da zai fuskanci Ferencvaros a Hungary.

Tuni kuma ya ajiye fitattun 'yan wasa uku da suka hada da Marc-Andre ter Stegen da Philippe Coutinho da kuma Lionel Messi da za su zauna a Spaniya.

'Yan kwallon da ke jinya a kungiyar ta Camp Nou sun hada da Gerard Pique da Sergi Roberto da Ronald Araujo da Samuel Umtiti da kuma Ansu Fati.

'Yan wasan Barcelona da za su fafata da Ferencvaros:

Net da, Inaki Pena da Arnau Tenas da Sergino Dest da Sergio Busquets da Carles Alena da Antoine Griezmann da Miralem Pjanic da Martin Braithwaite da kuma Ousmane Dembele.

Sauran sdun hada da Riqui Puig da Clement Lenglet da Pedri da Trincao da Jordi Alba da Matheus Fernandes da Frenkie de Jong da Junior Firpo da Oscar Mingueza da kuma Konrad de la Fuente.