Sai a wasan karshe za a tabbatar ko Real Madrid za ta kai zagayen gaba

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shakhtar ba ta ci wasa ba a cikin rukuni tun bayan da ta doke Real Madrid cikin watan Oktoba
An wallafa

Damar da Real Madrid keda ita na kai wa zagaye na biyu a Gasar Champions League na reto, bayan da Shakhtar Donetsk ta doke ta 2-0.

Real ta je Ukraine ne a wasa na biyar-biyar a cikin rukuni na biyu a gasar ta zakarun Turai ta shekarar nan ranar Talata.

A minti na 45 na farko da suka fafata sun je hutu ba ci, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Shakhtar ta ci kwallo biyunta.

Kuma Bruno Ferreira Bonfim ya ci na farko, sannan Manor Solomon ya kara na biyu.

A wasan farko da kungiyoyin biyu suka kara a cikin watan Oktoba, Shakhtar ce ta yi nasara da ci 3-2 a Spaniya.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta koma ta uku da maki bakwai, yayin da Shakhtar ta karbe mataki na biyu itama da makinta bakwai a rukuni na biyun.

Ranar 9 ga watan Disamba za a karkare karawar cikin rukuni, inda Real Madrid za ta karbi bakuncin Borussia Munchengladbach a Spaniya.

Da Real ta yi nasara a kan Shakhtar ranar Talata da tuni ta samu gurbin shiga wasannin zagaye na biyu a kakar bana.

'Yan wasa 21 da kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya fuskanci Shakhtar Donetsk.

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron baya: Militao da Varane da Nacho da Marcelo da Mendy da kuma Chust.

Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Odegaard da Isco da kuma Arribas.

Masu cin kwallo: Benzema da Asensio da Lucas V da Vini Jr. da Mariano da kuma Rodrygo.