An fara Gasar cin kofin Zakarun Afirka ta Champions League da ta Confederation

Caf Champions League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

A karshen mako aka fara wasannin zagayen farko na share fagen shiga gasar cin kofin Zakarun Afirka ta Champions League ta 2020/21.

Haka kuma a fara karawar zagayen farko a wasannin Zakarun Afirka ta Confederation Cup a dai karshen mako.

Ranar Juma'a Al Ahly ta lashe kofin Champions League na 2019/20, bayan da ta doke Zamalek da ci 2-1.

Wasannin bana sun ci karo da cikas din cutar korona, inda ake buga karawar ba yan kallo.

Tun cikin watan Maris annobar ta sa aka dakatar da dukkan wasanni a fadin duniya, in banda wasu kasashe da suka ci gaba da harkokinsu.

Kungiyar Enyimba ta Najeriya ta fara gasar bana da kafar dama, bayan da ta je Burkina Faso ta ci daya mai ban haushi.

Enyimba ta yi nasarar doke Rahimo ne, kuma Victor Mbaoma ne ya ci mata kwallon saura minti 14 a tashi daga karawar.

Ita kuwa Plateau United wadda ke wakiltar Najeriya ta yi rashin nasara a gida da ci 1-0 a hannun Simba ta Tanzaniya.

Za su buga karawa ta biyu tsakanin 4 zuwa 6 ga watan Disamba.

Sakamakon wasannin share fagen shiga gasar Zakarun Afirka ta bana:

  • Armed Forces (Gambia) 1-1 Teungueth (Senegal)
  • Racing Club Abidjan (Ivory Coast) 1-0 ASKO Kara (Togo)
  • AS Sonidep (Niger) 2-0 Mogadishu City Club (Somalia)
  • Forest Rangers (Zambia) 0-0 AS Bouenguidi (Gabon)
  • Jwaneng Galaxy (Botswana) 4-0 US Zilimadjou (Comoros)
  • Young Buffaloes (Eswatini) 0-0 Le Messager Ngozi (Burundi)
  • PWD Bamenda (Cameroon) 0-1 Kaizer Chiefs (South Africa)
  • AS Otoho (Congo) 1-1 Al Merrikh (Sudan)
  • Rahimo (Burundi) 0-1 Enyimba (Nigeria)
  • Nouadhibou (Mauritania) 1-1 Asante Kotoko (Ghana)
  • Vipers (Uganda) 0-1 Al Hilal (Sudan)
  • Buffles (Benin) 1-1 Mouloudia Alger (Algeria)
  • Mlandege (Zanzibar) 0-5 CS Sfaxien (Tunisia)
  • Bantu (Lesotho) 0-1 Nkana (Zambia)
  • Akonangui (Equatorial Guinea) 0-1 Petro Luanda (Angola)
  • Costa do Sol (Mozambique) 1-2 Platinum (Zimbabwe)
  • Plateau Utd (Nigeria) 0-1 Simba (Tanzania)
  • CR Belouizdad (Algeria) 2-0 Al Nasr (Libya)
  • APR (Rwanda) 2-1 Gor Mahia (Kenya)
  • AngloGold (Guinea) 1-2 Stade Malien (Mali)
  • Walkovers: Al Ahly Benghazi (Libya), Gazelle (Chad)

Sakamakon Confederation Cup karawar zagayen farko:

  • AS Kaloum (Guinea) 1-1 Tevragh-Zeina (Mauritania)
  • CI Kamsar (Guinea) 0-0 Renaissance (Chad)
  • Gamtel (The Gambia) 0-1 Tihad Casablanca (Morocco)
  • ASC Jaraaf (Senegal) 3-1 Kano Pillars (Nigeria)
  • Arta Solar 7 (Djibouti) 0-1 Al Mokawloon Al Arab (Egypt)
  • Al Ittihad (Libya) 4-1 Horseed SC (Somalia)
  • US Monastir (Tunisia) 2-0 Fasil Kenema (Ethiopia)
  • Namungo (Tanzania) 3-0 Al Rabita (South Sudan)
  • Orapa Utd (Botswana) 2-1 AS Kigali (Rwanda)
  • Ngazi Club (Comoros) 1-5 Napsa Stars (Zambia)
  • Etoile (Congo) 1-1 Bravos Maquis (Angola)
  • El Amal Atbara (Sudan) 1-0 KVZ (Tanzania)
  • AshantiGold (Ghana) 0-0 Salitas (Burundi)
  • Musongati (Burundi) 2-2 Green Eagles (Zambia)
  • Unisport Sokode (Togo) 0-2 Coton Sport (Camerooon)
  • Maniema Union (DR Congo) 0-2 Bloemfontein Celtic (South Africa)
  • Futuro Kings (Equatorial Guinea) 2-1 Rivers Utd (Nigeria)
  • Yeleen Olympique (Mali) 0-1 US Gendarmerie Nationale (Niger)
  • Walkover: Sagrada Esperanca (Angola)