Kasuwar cinikin 'yan kwallon kafa: Makomar Pepe, Messi, Mbappe, Haaland, Martinez, Coutinho

France's Kylian Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Arsenal ta shirya sayar da dan wasan Ivory Coast Nicolas Pepe idan aka samu kungiyar da za ta saye shi kan farashin da take son a biya ta don karbar dan wasan mai shekara 25, a cewar jaridar Daily Star on Sunday.

Babban abin daReal Madridta sanya a gaba yanzu shi ne daukar dan wasanParis St-Germain da Faransa mai shekara 21 Kylian Mbappe a 2021 sannan ta yi yunkurin dauko dan wasann Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20, daga Borussia Dortmund a 2022. (AS)

Chelsea tana "son dauko" dan wasan Argentina Lionel Messi mai shekara 33 idan ya bar Barcelona. (Spanish football expert Guillem Balague, via Sunday Express)

Dan wasanBarcadan kasar Sifaniya Gerard Pique, mai shekara 33, yana fatan Nou Camp za ta "ja hankali" Messi domin ya ci gaba da zama. (ESPN)

Shugaban Inter Milan Giuseppe Marotta ya ce mai yiwuwa dan wasan Denmark Christian Eriksen, mai shekara 28, zai bar kungiyar idan aka bude kasuwar cinikayyar 'yan kwallo a watan Janairu. (Sky Sports)

Wakilin dan wasan Brazil Philippe Coutinhoya ce dan wasan mai shekara 28 ba shi da niyyar barin Barcelona bayan da aka ce zai tafi Juventus. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Dan wasan Argentina Lautaro Martinez yana son barin Inter Milan kuma ya sa wakili Jorge Mendes ya dauki nauyin lalubo kungiyar da zai koma. (Marca)

Manchester City ta kwashe fiye da shekara daya tana bibiyar Martinez, inda ake rade radin cewa Barcelona da Real Madrid su ma suna son dan wasan mai shekara 23. (Sunday Mirror)

Bayanan bidiyo, Shin Messi zai iya shafe tarihin marigayi Maradona a duniyar ƙwallon ƙafa?