Kasuwar cinikin 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Haaland, Tagliafico, Kana, Bettinelli, Vydra

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban sashen wasanni na Borussia Dortmund, Michael Zorc ya ce yana ganin Erling Baraut Haaland, dan wasan gaba na kungiyar kuma dan Norway mai shekara 20 zai dade a kungiyar. Wa'adin kwantiragin Haaland sai 2024 za a sabunta ta, amma zai iya barin kungiyar idan wata kungiyar ta biya Dortmund euro miliyan 75 a 2022. (Bild Sport - in German)
Dan wasan baya na Argentina Nicolas Tagliafico, wanda ake tsammanin zai koma Chelsea ko Manchester City ya amince yayi zamansa a Ajax, wadda ke sa ran dan wasan mai shekara 28 zai yi zamansa a kungiyar a kalla zuwa karshen kakar wasan bana. (De Telegraaf - in Dutch)
Dan wasan baya na Liverpool Trent Alexander-Arnold mai shekara 22 ya soki yadda aka tsara jerin wasannin da kungiyoyi ke bugawa a wannan kakar wasan, yana cewa "hankali ma ba zai dauka ba.". (Evening Standard)
An umarci kungiyoyin kwallon kafa na Firimiyar Ingila da su rage yawan 'yan kallo da aka amince mu su da kada su zarce mutum 1,000. Hukumar da ke kula da lafiyar 'yan wasa da 'yan kallo ta ce sai an yi gwaji na wani lokaci kafin a amince mutum 2,000 su rika shiga filayen wasa. (Telegraph - subscription only)
Dan wasan baya na Anderlecht Marco Kana mai shekara 18 ya ce ba kungiyar da zai so komawa kamar Liverpool domin taka leda. (Walfoot, via Liverpool Echo)
Mai tsaron gida na Fulham Marcus Bettinelli mai shekara 28 na jan hankalin kungiyoyin Firimiyar Ingila. Dan wasan da a halin yanzu yake wasa a Middlesbrough, kocin kungiyar kwallon kafa ta Ingila Gareth Southgate ya kira shi a 2018 domin ya buga wa kasar wasa. (Mail)
Dan wasan Burnley kuma dan kasar Czech Matej Vydra mai shekara 28 na son barin kungiyar domin ya koma inda za a riga ba shi damar buga wasa a-kai-a-kai, . (Accrington Observer)
Tsohon kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya yi alkawarin ninka dukkan gudunmawar da aka tara wa wata gidauniya, kuma ya yi kira ga sauran 'yan kwallo da su tallafawa Marcus Rashford dan wasan United mai shekara 23 a kokarin da yake yi na kawar da yunwa a tsakanin kananan yara. (Times - subscription required)
Ma'aikatan kungiyar Gimnasia y Esgrima sun ajiye aikinsu. Kungiyar ce Diego Maradona ya horas kafin mutuwarsa. (Mail)











