Kasuwar cinikin 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Musah, Berge, Silva, Van Aanholt, Varane, Tevez

Valencia winger Yunus Musah

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Arsenal na sa do kan tsohon dan wasa Yunus Musah mai shekara 17, wanda sune suka raine shi tun yana karami, kuma Everton da Leeds da Wolves sun bayyana sha'awar sayen dan wasan da a yanzu ke buga wa Valencia, da kuma Amurka. (90 min)

Gunners din kuma na sha'awar sayo Sanda Berge, dan wasan tsakiya na Sheffield United duk da cewa sun gaza sayo dan wasan mai shekara 22 a watan Janairu bayan da ya koma Baramall Lane. (VG - in Norwegian)

Chelsea tuni ta fara tattaunawa da Thiago Silva, dan wasan baya mai shekara 36 domin ya tsawaita kwantiragin zamansa a kungiyar zuwa 2022. (Tuttomercato - in Italian)

Ajax na sha'awar sayo Patrick van Aanholt, dan wasan baya na Crystal Palace da Netherlands mai shekara 30 a watan Janairu ma zuwa. (Football Insider)

Real Madrid ta mayar da martani ga Raphael Varane bayan da aka ce Manchester United na sha'awar sayen dan wasan Faransar mai shekara 27, inda ta ce dan wasan "ba na sayarwa ba ne". (Sun)

Arsenal ta shirya tsaf domin tattaunawa da Nicolas Pepe mai shekara 25 bayan jan katin da aka ba shi a wasan da kungiyar ta buga da Leeds ranar Lahadi, sai dai da wuya su bayar da shi aro a watan Janairu. (Times - subscription only)

Bayern Munich ta yanke shawarar ba za ta tsawaita kwantiragin Jerome Boateng, dan wasanta dan kasar Jamus mai shekara 32 ba da zarar ta kare a cikin shekara mai shigowa. (Sport Bild - in German)

Inter Milan kuwa so ta ke ta sabunta kwantiragin Lautaro Martinez mai shekara 23 kafin a bude kasuwar cinikin 'yan wasa a watan Janairu, domin da alama Barcelona na sha'awar sayen dan wasan. (Sport)

Luka Modric mai shekara 35, kuma dan waasan Croatia ya bayyana sha'awarsa ta ci gaba da zama a Real Madrid bayan da kwantiraginsa ta kare a badi, kuma ya fi so ya yi ritaya a kungiyar. (Marca)

Dan wasan Real Madrid Isco mai shekara 28 na son barin Gasar La Liga. Dan kasar Sfaniyar ya taba nuna sha'awar komawa Ingila domin buga wasa a Gasar Firimiya. (La Cadena SER - in Spanish)