Jam'iyyar APC: Sabuwar rigima ta kunno kai a jam'iyya mai mulkin Najeriya

Mai Mala Buni
Bayanan hoto, Mai Mala Buni, shugaban riko na jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe
An wallafa

A Najeriya duk da yunkurin da kwamitin shugabancin wucin-gadi na jam'iyyar APC mai mulki ke cewa yana yi domin sasanta rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye jam'iyyar, ga alama har yanzu da sauran rina a kaba.

Dama Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya jagoranci kafa kwamitin domin sasanta 'ya'yan jam'iyyar bayan barakar da ta kunno a cikinta wadda ta kai ga cire shugabanta Adams Oshiomole daga mukaminsa a watannin baya.

Yanzu wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar dai sun yi kira ga kwamitin rikon kwaryar karkashin jagorancin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, da ya gudanar da babban taron jam'iyyar na ƙasa a watan gobe domin samun cikakkun shuwagabannin jam'iyya, idan ba haka ba kuma su ɗauki matakan ganin an rusa shi.

Suna dai zargin cewa - kwamitin yana wuce gona da iri - inda ya ɓuge da wasu ayyuka waɗanda ba su cikin nauyin da aka rataya masa, don dai ya ci gaba da jan ragamar jam'iyyar ta APC.

Ta yaya shuwagabannin rikon ke wuce gona da iri?

Daya daga cikin kusoshin jam'iyyar ta APC masu nuna rashin gamsuwa da tafiyar jam'iyyar a yanzu, Sanata Kabiru Marafa, ya ce kwamitin na wuce gona da iri.

Sanata Marafa wanda ya taba neman yi wa jam'iyyar takarar kujerar gwamna a jihar Zamfara, ya ce aikin da kwamitin ke yi na yin rajistar 'ya'yan jam'iyya a fadin kasar ya saba ka'idar aikin da aka ba shi.

Ya shaida wa BBC cewa yin rajistar ba ya cikin aikin da aka ba kwamitin rikon kwaryar inda ya kara da cewa ''Abin da aka ba ku ku je ku yi, babu wannan rajistar a ciki. Kuma yin rajistar nan zai kara kawo baraka a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar''

To sai dai wani jigo a jam'iyyar ta APC kuma tsohon mai bai wa shugaba Buhari shawara kan lamuran majalisa, Hon. Kawu Sumaila, ya ce aikin kwamitin na yin rajistar 'yan jam'iyya na kan turba domin dama bisa tsarin jam'iyyar wajibi ne duk bayan kimanin shekaru shida a sake sabunta rajistar 'yan jam'iyyar domin 'tantancewa da tabbatar da halin da 'yan jam'iyya da suke ciki''.

Kawu Sumaila ya ce wannan na cikin aikin da aka bai wa kwamitin na Mai Mala Buni.

Rikicin cikin gidan dai na daya daga cikin manyan matsaloli da ke kawo wa jam'iyyar ta APC mai mulkin Najeriya cikas, inda a baya-bayan nan ta sha kaye a zaben gwamnan jihar Edo a hannun jam'iyyar hamayya ta PDP.

Wakilin BBC Zaharaddeen Lawan ya ce ga alama dalilan rigingimun cikin gida da jam'iyar ke fuskanta sun har da kulle-kullen manyan zabukan 2023, lokacin da ake sa ran wa'adin mulkin shugaba Muhammadu Buhari zai cika.

A ranar Alhamis ne aka rantsar da gwamnan jihar Yobe, Alhaji Maimala Buni a matsayin shugaban kwamitin sulhu na APC

Asalin hoton, BUHARI SALLAU

Bayanan hoto, A ranar Alhamis ne aka rantsar da gwamnan jihar Yobe, Alhaji Maimala Buni a matsayin shugaban kwamitin sulhu na APC

'Ba zamu zabi sabbin shuwagabannin jam'iyya yanzu ba'

Masu korafi kan salon aikin kwamitin rikon kwaryar na cewa kamata ya yi kwamitin ya shirya babban taron jam'iyya na kasa domin zaben shuwagabanni masu cikakken iko da wa'adin mulki su tafiyar da jam'iyyar.

Suna cewa rashin yin, hakan zai iya yin karan tsaye ga jam'iyyar. To sai dai duk da kiraye-kiraye da wasu 'yan jam'iyyar ke yi na a samar da cikakkun shuwagabanni, jam'iyyar ta APC ta ce ba zata gudanar da zaben sabbin shuwagabanni a yanzu ba.

Wata sanarwa da kakakin jam'iyyar na kasa Yekini Nabena ya fitar, ta ce ba za a yi babban taron jam'iyya ba sai an dinke barakar da ke cikin jam'iyyar.

Shi ma Honourable Kawu Sumaila ya ce ba za a yi zabukan shuwagabannin jam'iyya ba sai a samu nasarar sasantawa, da kuma yin sabuwar rajistar 'ya'yan jam'iyyar.

Sanarawar jam'iyyar APC ta ce kawo yanzu an samu ci gaba wajen aikin sulhunta 'ya'yan jam'iyyar a wasu jihohin kasar.

Dambarwar za ta iya danganawa da kotu

Hedikwatar jam'iyyar APC ta kasa dai ta ce kwamitin rikon kwaryar wanda babban aikinsa shi ne sulhu a cikin jam'iyyar, ya samu nasarar sasanta 'ya'yan jam'iyyar a jihohin da suka hada da: Bauchi, Cross River, Edo, Ekiti, Enugu, Ondo, Oyo da kuma Zamfara.

To sai dai jigo a jam'iyyar ta APC da ya fito daga jihar Zamfara, Sanata Kabiru Marafa, ya ce ba a yi aikin sasantawa a jihar Zamfara ba domin a matsayinsa na mai rike da bangare guda na jam'iyyar amma ba a tuntube shi ba.

Ya kuma ce muddin za a yi sulhu a jihar Zamfara, to dole ne a tuntube shi domin yana cikin wadanda aka 'muzguna' masu. ''Ni ban ce ba wani wanda za a yi sasanci da shi ba, amma ni ina cikin wadanda lallai-lallai dole ne a yi sasanci da ni, domin an muzguna mun kuma an yi mun abin da ba daidai ba.''

Game da batun wuce gona da iri da suke zargin kwamitin riko na jam'iyyar ke yi, Sanata Marafa ya ce muddin kwamitin bai daina yin aikin da ba a bashi ba, to za su garzaya kotu domin kalubalantar kwamitin. Bai dai bayyana ko zuwa yaushe ne za su shigar da karar ba.

To amma yayin da yake kare aikin kwamitin musamman na yin sabuwar rajista,

Tshohon mai bai wa shugaba Buhari shawara kan lamuran majalisar dokoki, Sulaiman Kawu Sumaila, ya ce kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya ba kwamitin ikon sabunta rajistar.

Ya kuma ce tabbas har yanzu akwai sauran baraka a jam'iyyar amma ya bayyana fatan za a dinke ta. Ya kuma ce sabunta rajistar na daya daga cikin matakan farko da suka wajaba kafin gudanar da zabukan shuwagabanni a dukkan matakai na shugabanci.

Wasu masharhanta dai na ganin wannan rikici na cikin gida da jam'iyyar APC mai mulki ke fama da shi, ka iya bin ta har zuwa manyan zabuka na 2023 musamman idan aka yi la'akari da irin muradu daban-daban dake cikin jam'iyyar da kuma yadda wasu ke ci gaba da nuna rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da lamuranta.