Ahmed Musa ya bar ƙungiyar Al Nassr ta Saudiyya

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Najeriya Ahmad Musa ya bar ƙungiyar Najd Knight bayan kwashe shekara biyu da kulob din da ya lashe gasar Saudiyya sau takwas.
Kungiyar ta bayyana tafiyar dan wasan ne a shafinta Twitter.
Musa mai shekara 28 yanzu ba shi da wata ƙungiya sai dai rahotanni na cewa yana son koma wa Turai ne da taka leda bayan barin ƙungiyar cikin ruwan sanyi.
Cikin wani saƙo da ta wallafa, ƙungiyar ta haɗa wani hoton bidiyo tun daga farkon zuwansa har da ƙwallayen da ya jefa, tare da yi masa fatan alheri a rayuwar ƙwallonsa a nan gaba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
"Mun gode tauraron Najeriya muna maka fatan alkhairi a rayuwarka ta gaba Ahmed Musa!," Al Nassr ta wallafa.
Bayan kammala zamansa na aro na shekara biyu CSKA Moscow, dan wasan Najeriyar ya koma Al Nassr kan kwantaragin shekara hudu daga Leicester City.
Al Nassr ta doke da yawa daga cikin ƙungiyoyin Turai a rige-rigen ɗaukar tsohon ɗan wasan, wanda ya taka rawar a zo a gani a Gasar cin Kofin Duniya na 2018 a Rasha ta hanyar cin ƙwallo biyu a wasa uku.

Asalin hoton, Getty Images
Cikin wasa 58 da ya bugawa ƙungiyar, ya samu nasarar jefa ƙwallo 11 da kuma bayar da 14 aka ci, ya kuma taimaka wa ƙungiyar ta ɗauki kofin gasar ƙasar da kuma Super Cup ɗinta.
Yanzu dai ana sanya ido domin jin inda ɗan wasan zai nufa a rayuwarsa ta gaba a ƙwallon kafa.











