Benzema ya buga wa Madrid wasa na 350 a La Liga

An wallafa

Ranar Lahadi Real ta ziyarci Sociedad a wasan makon farko a La Liga ta bana, inda Karim Benzema ya buga karawar kuma ta 350 da ya yi a gasar kenan.

Sai dai kungiyoyin sun tashi wasan babu ci, kuma karo na biyar kenan da Madrid kan yi canjaras a wasan farko a La Liga daga takwas baya da ta yi.

Benzema wanda ke shekara ta 12 a Santiago Bernabeu, ya fara taka leada ranar 9 ga watan Yulin 2009.

Tsahon lokacin da ya kwashe yana buga tamaula a Real, Benzema ya nuna kansa a matakin mai zura kwallaye a raga.

Wadanda ke gabansa a zura kwallaye a raga a Madrid a La Liga sun hada da Cristiano Ronaldo mai 312 da Raúl mai 228 da Di Stéfano mai 216 da kuma Santillana wanda ya zi 186.

Benzema wanda ya zura kwallo 169 a La Liga ya kuma ci wa Madrid kwallo 249 a dukkan fafatawar da ya yi kuma shi ne na biyar kan sharara kwallaye a Real.

Dan wasan tawagar Faransa shi ne na uku a jerin bakin da suka buga wa Real wasannin La Liga da dama, bayan Roberto Carlos mai 370 da kuma Marcelo da ya yi karawa 358.

Haka kuma Benzema yana cikin 'yan wasan da Real ta yi nasara a gasar La Liga sau 246 da yin canjaras 56 da rashin nasara 48.

Benzema ya lashe kofin La Liga uku da suka hada a kakar 2011/12 da 2016/17 da kuma ta 2019/20.