Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Benzema ya ci kwallo 135 a Santiago Bernabeu
A ranar Asabar Real Madrid ta karbi bakuncin Granada a gasar cin kofin La Liga wasan mako na takwas da suka fafata a Santiago Bernabeu.
Real ce ta yi nasara da ci 4-2 a wasan, kuma wadanda suka ci mata kwallayern sun hada da Karim Benzema da Eden Hazard da Luka Modric da kuma James Rodriguez.
Kwallon da Benzema ya ci a gumurzun shi ne na 135 ya ci wa Madrid kwallo a Santiago Bernabeu.
Dan kasar Faransa ya fara cin kwallo a karawar da Real ta yi da Xerez a cikin watan Satumbar 2009.
Kawo yanzu ya ci kwallo 73 a gasar La Liga da 19 a Champions League da bakwai a Copa del Rey da guda daya da ya ci a Spanish Super Cup.
Haka kuma sau biyar yana cin kwallo uku-uku rigis a filin na Bernabeu da ya hada da wadda ya ci Auxerre da Malmo a gasar cin kofin Zakaraun Turai ta Champions League.
Da kuma ukun da ya ci Rayo Vallecano da Athletic a gasar La Liga da kuma Levante a Copa del Rey.
A kakar 2011/12 Benzema ya fi cin kwallaye da dama a gida, wanda ya ci 25 jumulla a Santiago Bernabeu.
Kawo yanzu Benzema ya ci wa Real Madrid kwallo 228 a kaka 11 da ya yi a kungiyar, kuma shi ne na shida a jerin wadanda suke kan gaba wajen ci mata kwallaye a tarihi.
Cikin dukkan karawar da Benzema ya yi wa Real ya ci mata kwallo 99 a La Liga da 26 a Champions League da tara a Copa del Rey da guda daya a Spanish Super Cup.