Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Benzema ya buga Champions League 100 a Real
Karim Benzema ya yi wa Real Madrid wasa 100 a Champions League ranar Laraba a Santiago Bernabeu.
Sai dai kuma a karawar ta 100 da ya buga wa Real ta yi rashin nasara a karon farko a hannun Manchester City da ci 2-1 a wasan zagaye na biyu.
Wannan ne karon farko da Manchester City ta yi nasara a kan Real Madrid a gasar Champions League.
Dan wasan tawagar Faransa yana kaka ta 11 a Real Madrid, kuma shi ne na uku a jeren wadanda suka ci wa kungiyar kwallaye a Champions League mai 52 a raga.
Cikin wasa 100 da Benzema ya yi wa Madrid an yi nasara da shi a fafatawa 66, ya kuma lashe Champions League hudu.
A shekarar 2016/17 ya zama dan wasan da ke kan gaba wajen buga wasannin Zakarun Turai a Real wadda ta cin kakar, shi kuma ya yi wasa 13.
A kakar bana ya buga karawa bakwai, ya kuma ci kwallo a fafatawa da Galatasaray da kuma PSG.
Sau takwas yana fuskantar Bayern Munich a Champions League a wasa 100 da ya yi, kuma ya buga nasara shida da Real ta yi a kan Ajax.
Galatasaray ce ya fi zura wa kwallo, inda ya ci biyar, ya kuma ci Auxerre kwallo uku a 2010/11 da Malmo a 2015/16.
Ya kuma ci kwallo a fafatawar da Real Madrid ta ci Liverpool ta lashe kofin Champions League.
Real Madrid za ta ziyarci Manchester City a wasa na biyu da za su kara a Etihad ranar 17 ga watan Maris.