Barcelona: Ƙungiyar na son ɗauko tsohon ɗan wasanta Koemna

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Barcelona na ƙoƙarin maye gurbin tsohon kocinta da ta kora Quique Setien da kocin Netherland Ronald Koeman.
Ƙwararren masanin gasar Spaniya Gullam Blag ya ce an tattauna da tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino, sai dai tsohon dan wasan Barcelona Koeman aka fi mayar da hankali akai.
Barcelona ta kori kocin nata Setien bayan wulaƙancin da Bayern Munich ta yi mata a Gasar Zakarun Turai, na kora ta gida da ruwan kwallaye 8-2.
Kocin ya gaza ɗaukar Gasar Spaniya ta 2019-20 wadda ya daɗe yana jan ragamar ta daga farko.
Setien mai shekaru 61 an ɗauko shi ne a matsayin haya ya kuma maye gurbin Ernesto Valverde a watan Janairu.







