Arsenal tana fuskantar ƙalubale kan Ceballos, Manchester United na son Chiesa

Dani Ceballos

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Arsenal tana fuskantar kalubale daga wurin AC Milan, Valencia da kuma Real Betis a kan dan wasan tsakiya Dani Ceballos, mai shekara 23, idan tana so ta mayar da zaman aron da dan wasan na Sufaniya da ta karbo daga Real Madrid ya zama na dindindin. (Express)

Manchester United tana dab da kammala kulla yarjejeniya da Fiorentina kan dan wasan Italiya Federico Chiesa, mai shekara 22. (Corriere Fiorentino via Star)

Chelsea ta matsa kaimi a yunkurinta na dauko dan wasan Jamus da Bayer Leverkusen Kai Havertz, mai shekara 21, saboda dan wasanta dan kasar Ingila Callum Hudson-Odoi, dan shekara 19, bai taka rawar ganin da ta yi tsammani daga gare shi ba. (90min)

Barcelona ta kulla yarjejeniya da dan wasan Inter Milan daArgentina Lautaro Martinez, mai shekara 22, ko da yake yarjejeniyar ta ta'allaka ne da idan Milan za ta iya sayar da dan wasan Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 28, wanda ya kwashe kakar wasan bana yana zaman aro a Bayern Munich. (ESPN)

Daraktan wasanni naWerder Bremen Frank Baumann ya tabbatar cewa dan wasan Kosovo Milot Rashica ya nemi barin kungiyar a bazara, inda raotanni suka ce Wolves, Liverpool, AC Milan, RB Leipzig da kuma Hertha BSC suna son daukar dan wasan mai shekara 24. (Werder Bremen via Bundesliga News)

Dan wasan Amurka Weston McKennie yana shirin barin Schalke inda aka ce kungiyoyin Turai da dama, cikinsu har da Liverpool da Chelsea, suna son dauko dan wasan. (CBS Sports)

Har yanzu dan wasan Arsenalmai shekara21 Matteo Guendouzi yana atisaye shi kadai saboda kocin kungiyar Mikel Arteta bai yanke shawarar sanya shi a tawagar farko ba. (ESPN)

Chelsea tana bibiyar irin ci gaban da dan wasan Monaco dan kasar Faransa Malamine Efekele, dan shekara 15, yake samu. (L'Equipe via Mail)

Dan wasan Everton da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo Yannick Bolasie, mai shekara 31, ya ce yana son ci gaba da zama a kungiyar kuma ya buga wasa gaban Carlo Ancelotti, bayan ya koma daga zaman aro a Sporting Lisbon. (Liverpool Echo)

Barcelona ce kan gaba a yunkurin dauko dan wasan Sufaniya Fabian Luzzi, dan shekara 16, daga Rayo Vallecano, a yayin da kungiyoyin Turai da dama ke zawarcinsa. (Marca)