Jordan Henderson: Kyatin ɗin Liverpool zai yi jinya har ƙarshen kakar wasan bana

Liverpool midfielder Jordan Henderson

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Henderson ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin Liverpool ta yi nasarar lashe gasar Firimiya
An wallafa

Kyaftin ɗin Liverpool Jordan Henderson ba zai buga wasanni huɗu da suka rage a kakar wasan bana ba saboda raunin da ya ji a gwiwarsa, a cewar manajan ƙungiyar Jurgen Klopp.

Henderson ya zura kwallo a wasan da suka doke Brighton da ci 3-1 ranar Laraba kafin ya soma ɗingishi a kusan ƙarshen wasan.

Klopp ya ce ɗan wasan na Ingila zai samu sauƙi domin a soma kakar wasan 2020-21 da shi.

Henderson, mai shekara 30, wanda ya taka muhimmiyar rawa a lashe kofin Firimiya da Liverpool ta yi, ba zai buƙaci a yi masa tiyata ba.

Bayanan bidiyo, "Lamarin babu daɗi amma hakan ne kawai ya fiye mana, in ji Klopp

"Lamarin babu daɗi amma hakan ne kawai ya fiye mana," a cewar Klopp ranar Juma'a.

A watan jiya Liverpool ta lashe kofin Firimiya wanda ta kwashe shekara 30 tana jira kuma Klopp ya ce raunin da Henderson, wanda ya buga wasa 30 a kakar da ta wuce ya yi, ba zai hana shi ɗaga kofin Firimiya a wasan da za su yi da Chelsea ranar 22 ga watan Yuli ba.