Jordan Henderson: Kyatin ɗin Liverpool zai yi jinya har ƙarshen kakar wasan bana

An wallafa

Kyaftin ɗin Liverpool Jordan Henderson ba zai buga wasanni huɗu da suka rage a kakar wasan bana ba saboda raunin da ya ji a gwiwarsa, a cewar manajan ƙungiyar Jurgen Klopp.

Henderson ya zura kwallo a wasan da suka doke Brighton da ci 3-1 ranar Laraba kafin ya soma ɗingishi a kusan ƙarshen wasan.

Klopp ya ce ɗan wasan na Ingila zai samu sauƙi domin a soma kakar wasan 2020-21 da shi.

Henderson, mai shekara 30, wanda ya taka muhimmiyar rawa a lashe kofin Firimiya da Liverpool ta yi, ba zai buƙaci a yi masa tiyata ba.

"Lamarin babu daɗi amma hakan ne kawai ya fiye mana," a cewar Klopp ranar Juma'a.

A watan jiya Liverpool ta lashe kofin Firimiya wanda ta kwashe shekara 30 tana jira kuma Klopp ya ce raunin da Henderson, wanda ya buga wasa 30 a kakar da ta wuce ya yi, ba zai hana shi ɗaga kofin Firimiya a wasan da za su yi da Chelsea ranar 22 ga watan Yuli ba.