Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City za ta fafata da Madrid a Etihad a Champions League:
An amince wa Manchester City ta buga gasar Champions League karawa ta biyu da za ta fafata da Real Madrid a Etihad.
Hukumar kwallon kafa ta Turai ta tabbatar cewar duk wasan da suka yi kwantai a Champions League da Europa za a buga su kamar yadda aka tsara sai dai ba 'yan kallo.
Man City za ta karbi bakuncin Real tsakanin 7 ko 8 ga watan Agusta, yayin da Chelsea za ta ziyarci Bayern Munich a wasanni kungiyoyi 16 da suka rage a gasar bana.
An dakatar da wasannin cin kofin Zakarun Turai a cikin watan Maris sakamakon bullar cutar korona, bayan da an buga karawar zagayen farko.
City ta yi nasara a kan Real Madrid a wasan farko a Spaniya da ci 2-1, ita kuwa Chelsea rashin nasara ta yi a Stamford Bridge da ci 3-0 a hannun Bayern Munich.
A gasar Europa kuwa Wolverhampton za ta karbi bakuncin Olympiokos, haka ita ma Manchester United za ta yi wa LASK masauki tsakanin 5 ko 6 ga watan Agusta.
Manchester United ta ci 5-0 a gidan LASK, Wolves kuwa 1-1 ta buga a Girka, yayin da Rangers za ta je gidan Bayern Leverkusen.
Wasan Inter Milan da Getafe da na Sevilla da Roma za a kara sau daya ne a Jamus, saboda yanayin cutar korona da ta yi tsamari a Italiya da kuma Spaniya.
Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai ta kuma ce dukkan wasannin daf da na kusa da na karshe zuwa na karshe za a buga su ba 'yan kallo.
Za a fara karawar daf da na kusa da na karshe da wasan daf da karshe da na karshe a Champions League daga 12 zuwa 23 ga watan Agusta a Lisbon.
Filayen wasanni a Jamus ne za su karbi bakuncin wasannin Europa League har da karawar karshe da za a yi ranar 21 ga watan Agusta a Cologne.
Ranar Juma'a ake sa ran fitar da jadawalin gasar Champions League da ta Europa League.
Haka ma gasar kwallon mata ta Champions League za a buga ziri daya kwale a Arewacin Spaniya tsakanin 21 zuwa 30 ga watan Agusta.