Chelsea ta koma matakinta na hudu a teburin Premier

Olivier Giroud

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Olivier Giroud ya ci kwallo biyu a wasa uku da aka fara da shi tun da aka ci gaba da buga gasar Premier League
An wallafa

Kungiyar Chelsea ta doke Watford da ci 3-0 a gasar Premier League karawar mako na 33 da suka buga ranar Lahadi a Stamford Bridge.

Chelsea ta ci kwallon farko ta hannun Olivier Giroud a minti na 28 da fara wasa.

Kungiyar ta Stamford Bridge ta zura na biyu a bugun fenariti ta hannun Willian, sannan Ross Barley ya ci mata na uku.

Da wannan sakamakon Chelsea ta koma matakinta na hudu a kan teburin Premier da maki 57.

Haka kuma kungiyar ta Stamford Bridge ta yi nasara a karawa uku daga hudun da ta bugu tun lokacin da aka ci gaba da buga gasar Premier.

Tun kan wasan Chelsea, Manchester United ta doke Bournemouth da ci 5-2 ta dare gurbi na hudun da maki 55.

Yanzu United ta koma ta biyar kenan, bayan buga wasanni 33 a gasar shekarar nan.

A wasan da ya gabata ne Chelsea ta yi rashin nasara a karawar hamayya a gidan West Ham da ci 3-2 ranar Alhamis.

Chelsea za ta ziyarci Crystal Palace a wasan gaba ranar Talata, yayin da Watford wadda take cikin 'yan kasan teburi za ta karbi bakuncin Norwich City a dai ranar.