Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta koma matakinta na hudu a teburin Premier
Kungiyar Chelsea ta doke Watford da ci 3-0 a gasar Premier League karawar mako na 33 da suka buga ranar Lahadi a Stamford Bridge.
Chelsea ta ci kwallon farko ta hannun Olivier Giroud a minti na 28 da fara wasa.
Kungiyar ta Stamford Bridge ta zura na biyu a bugun fenariti ta hannun Willian, sannan Ross Barley ya ci mata na uku.
Da wannan sakamakon Chelsea ta koma matakinta na hudu a kan teburin Premier da maki 57.
Haka kuma kungiyar ta Stamford Bridge ta yi nasara a karawa uku daga hudun da ta bugu tun lokacin da aka ci gaba da buga gasar Premier.
Tun kan wasan Chelsea, Manchester United ta doke Bournemouth da ci 5-2 ta dare gurbi na hudun da maki 55.
Yanzu United ta koma ta biyar kenan, bayan buga wasanni 33 a gasar shekarar nan.
A wasan da ya gabata ne Chelsea ta yi rashin nasara a karawar hamayya a gidan West Ham da ci 3-2 ranar Alhamis.
Chelsea za ta ziyarci Crystal Palace a wasan gaba ranar Talata, yayin da Watford wadda take cikin 'yan kasan teburi za ta karbi bakuncin Norwich City a dai ranar.