'Yan Real da za su bakuncin Espanyol a La Liga

An wallafa

Espanyol za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan mako na 32 a gasar La Liga, tuni Real ta bayyana 'yan wasan da za su buga mata karawar ranar Lahadi.

A wasan farko da suka kara cikin Disambar 2019, Madrid ce ta yi nasara da ci 2-0 a fafatawar da suka yi a Santiago Bernabeu.

Real ta fara cin kwallo ta hannun Raphael Varane tun kan hutu, bayan da suka koma zagaye na biyu ne da wasa ya nutsa sai Karim Benzema ya kara na biyu.

A kuma gumurzun Real Madrid ta karasa wasan da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Ferland Mendy jan kati saura minti bakwai lokaci ya cika.

Real Madrid wacce ta yi wasa 31 tana ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki daya, bayan da Barcelona mai karawa 32 ta buga 2-2 da Espanyol ranar Asabar.

Idan Real Madrid ta doke Espanyol ranar Lahadi za ta dare kan teburin La Liga da tazarar maki biyu tsakaninta da Barcelona.

Tuni kuma kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasa 23 da za su fuskanci Espanyol.

'Yan wasan Real da aka je da su Espanyol:

Masu tsaron raga: Courtois da Areola da kuma Altube.

Masu tsaron baya: Carvajal da Militão da Ramos da Varane da Marcelo da Javi Hernández da Miguel Gutiérrez.

Masu buga tsakiya: Kroos da Casemiro da Valverde da kuma James, Isco.

Masu buga gaba: Hazard da Benzema da Bale da Asensio da Brahim da Mariano da Vinicius Jr. da kuma Rodrygo.