Gareth Bale ya buga wa Real Madrid wasa na 250

An wallafa

Gareth Bale ya buga wa Real Madrid wasa na 250 a karawar da kungiyar ta doke Eibar 3-1 ranar Lahadi a gasar La Liga wasan mako na 28.

Dan wasan tawagar Wales wanda ke kaka ta bakwai a Real an ci wasa 162 da shi ya kuma ci wa kungiyar kwallo 105.

Cikin karawa 250 da ya yi wa Real Madrid ya buga wasannin La Liga 170 Champions League 55 da Copa del Rey 13 da kofin zakarun nahiyoyin duniya wato Club World Cup wasa 6 da Spanish Super karawa uku da kuma European Super Cup wasa uku, sannan ya buga fafatawa 19 a kakar bana.

Kakar da Bale ya fi buga wa Real wasa ita ce ta 2014-15 wadda ya yi 48. Wasannin da ya fi buga wa shi ne na hamayya sau 20, kuma kungiyar da ya fi ci ita ce Real Sociedad har karo tara.

Cikin kwallo 105 da ya ci sun hada da 80 a La Liga da 16 a Champions League da 6 a Club World Cup da kuma 3 a Copa del Rey.

Wasannin da ya fi bajinta sun hada da kwallo hudu da ya zura a ragar Rayo Vallecano a kakar 2015/16 da kuma uku rigis da ya ci Valladolid a kakar 2013/14 da Deportivo de La Coruna a kakar 2015/16 da kuma Kashima Antlers a kakar 2018/19.

Bale ya kuma ci wa Madrid kwallayen raba gardama a fafatawa uku da zumullar kwallo hudu a raga kuma a wasan karshe.

Shi ne ya ci biyu a Champions League da Real ta doke Liverpool ya kuma ci San Lorenzo a Club World Cup a 2014/15 da kuma wadda ya zura a ragar Barcelona a Copa del Rey a 2013/14.