Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid ta ci wasa na 1,100 a gida a gasar La Liga
Real Madrid ta zama ta farko da ke da yawan cin wasan La Liga a gida, bayan da ta doke Real Mallorca kuma shi ne na 1,100 da ta yi nasara.
Jumulla Real ta yi wasan gasar La Liga 1,435 a gida da canjaras 205 da rashin nasara a wasa 130.
Wacce take biye da Real Madrid a yawan cin wasa a gida ita ce Barcelona da nasara 1,095.
Real ta yi wasan La Liga a bana ba a doke ta ba a gida, bayan da ta ci wasa 12 da canjaras 4.
Kakar da Real ta fi taka rawar gani a gida a La Liga ita ce ta 1987/88 da kuma 2009/10, inda ta ci wasa 18 ta kuma ci kwallaye 3,833 a lokacin.
Real Madrid wacce take da maki iri daya da na Bacelona ta koma ta daya a kan teburin La Liga, bayan da ta doke Real Mallorca 2-0.
Ranar Asabar 27 ga watan Yuni, Barcelona za ta ziyarci Celta de Vigo a wasan mako na 32.
Sai a ranar Lahadi 28 ga watan Yuni, Espanyol za ta karbi bakuncin Real Madrid.