Leroy Sane: Dan wasan Man City yana son barin kungiyar, in ji Pep Guardiola

An wallafa

Leroy Sane yanason barin Manchester City, in ji kocin kungiyar Pep Guardiola.

City ta yi kokarin ganin ta rarrashi dan kasar Jamus ɗin mai shekara 24 ya tsawaita kwangilarsa, wacce za ta kare a 2021.

Sai dai Sane, wanda aka kwashe shekara daya ana rade radin zai koma Bayern Munich, ya yi watsi da tayin komawa kungiyoyi da dama.

"Yana son komawa wata kungiyar," a cewar Guardiola. "Ban sani ba ko zai bar mu a wannan bazarar ko bazara mai zuwa idan kwangilarsa ta kare."

A 2016 Sane ya sanya hannu kan kwangilar shekara biyar da City daga Schalke a kan £37m.

Bai buga wa kungiyar wasa ba tun da ya ji rauni a cinyarsa a watan Agusta lokacin gasar Community Shield.

Guardiola ya ce City ta yi magana da Sane "sau biyu zuwa uku" a kan sabunta kwangilarsa, inda ya kara da cewa: "Idan muka nemi sabunta kwangilar dan wasa muna yi ne domin muna son sa.

"Yana da dabi'u masu kyawu. Muna son 'yan wasan da ke son buga tamaula a kungiyar don cimma muradunmu.