Polio: WHO tana gab da bai wa Najeriya shaidar rabuwa da cutar

Shan-inna

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce ta amince da takardun neman shaidar rabuwa da cutar shan-Inna wato Polio da kasashen Najeriya da Kamaru da Sudan ta Kudu da kuma Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka suka gabatar mata.

WHO ta ce takardu da kuma bayanan da kasashen na Afirka suka gabatar sun cika dukkan sharudan ayyana su a matsayin wadanda ba su da cutar polio, amma dai ana bukatar karin bitar yanayin da suke ciki kafin a bayar da sanarwa ta karshe kan matsayinsu game da cutar mai nakasa yara.

WHO ta ce wannan wani lokaci mai cikke da tarihi ga Afirka da kuma yunkurin kawar da cutar ta Shann Inna daga doron kasa.

Sai dai kuma Hukumar bayar da shaidar rabuwa da polio ta Sashen Afirka za ta sake duba bayanan da kasashen suka gabatar, ana kuma sa ran hukumar bada shaidar mai zaman kanta ta zata bai wa nahiyar Afirka shaida ta rabuwa da polio a cikin watan Agusta, bayan an kammala tsare-tsaren masu wuyan sha'ani.

Muddin a karshe aka ayyna Afirka a matsayin wadda ta rabu da cutar polio, haka zai kasance wata muhimmiyar gaba a yunkurin kawar da cutar a fadin duniya.

Nau'in ciwon na asali dai shi ne wanda duniya ta fi damuwa ta kawar dai shi.

Da ma kasashen Najeriya da Afghanistan da Pakistan ne suka rage a duniya masu wannan nau'in a duniya a cewar WHO, amma kusan shekaru hudu ke nan Najeriya ba ta sake samun shi wannan nau'in ba abinda ya kawo ta ga matakin na gab da samun shaida rabuwa da ita.

Yanzu Afghanistan da Pakistan suka rage a duniya. To sai dai kuma wasu kasashen Afirka na da wani nau'in cutar na daban, wanda ake samu a yanayin da ba a yi riga-kafi yadda yakamata ba, ko kuma wanda ya ke rikida a cikin ruwan rigakafin da ake bayarwa wanda ake kira vaccine derived polio.

Galibi dai cutar shan-Inna kananan yara take kamawa, kuma ba ta da magani.

Amma dai tana da riga-kafi.

Kafin a ayyana kasa ko nahiya a matsayin wadda ta rabu da cutar polio sai ta kwashe akalla shekaru uku a jere ba tare da wani ya kamu da cutar ba, sannan ta tanadi gamsasshen tsarin sa ido da kuma shirin ko ta kwana na tunkarar barkewar cutar a gaba.