Zan kara sa kwazo a Chelsea - Olivier Giroud

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan tawagar kwallon kafar Faransa, Olivier Giroud ya ce zai ci gaba da sa kwazo a wasannin da zai buga wa Chelsea.
Cikin watan Mayu ne Giroud ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara daya da za ta kare a karshen kakar badi.
Giroud ya buga wasan Premier League biyar a watan Janairu a lokacin saura wata shida suka rage kwantiraginsa ya kare a Chelsea.
Sai dai bayan da Tammy Abraham ya yi rauni ne kocin Chelsea, Frank Lampard ya ke amfani da Giroud, wanda ya ci kwallo biyu a wasa hudu a Premier.
Giroud ya ce ''Da cikin watan Janairu ya kamata na bar Stamford Bridge, saboda bana buga wasanni sosai, amma yanzu ina son nuna kwarewata don na buga wa Faransa Euro 2020''.
Giroud mai shekara 33, ya koma Chelsea a Janairun 2018, ya buga mata wasa 39 da 37 da ya yi canji ya kuma ci kwallo 21 kawo yanzu.
Dan wasan tawagar Faransa shi ne ya ci wa Chelsea kwallo na karshe a wasan da suka doke Everton 4-0 ranar 6 ga watan Maris daga nan aka dakatar da wasanni saboda bullar cutar korona.
Ranar 17 ga watan Yuni za a ci gaba da wasannin Premier League, kuma Chelsea tana mataki na hudu a kan teburi.











