Chelsea ta umarci 'yan wasan da suka je gida su koma Ingila ranar Lahadi

Chelsea's Christian Pulisic and Emerson

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Christian Pulisic da Emerson na daga cikin 'yan wasan Chelsea da ta bukaci su koma Ingila nan da ranar Lahadi
An wallafa

Chelsea ta umarci dukkan 'yan wasanta da suka je gida hutu da su koma Ingila nan da Lahadi, saboda shirin ci gaba da gasar Premier da ake yi.

Chelsea ta bar 'yan wasa da dama sun koma gida ciki har da dan kwallon Brazil, Willian, tun bayan bullar cutar korona da ta sa aka dakatar da wasanni Premier ranar 13 ga watan Maris.

Ana sa ran watakila a koma ci gaba da Premier na bana cikin watan Yuni, inda Chelsea ke son yin shiri tun kan lokacin.

A ranar Juma'a kungiyoyin da ke buga gasar Premier da mahukunta da masu ruwa da tsaki za su yi taro ta bidiyo kan hanyoyin da ya kamata a tsara don karkare kakar 2019-20.

Chelsea za ta daga kafa ga wadanda ba su samu damar komawa Ingila ranar Lahadi ba, don ta kwan da sanin tafiye-tafiye zai yi wahala, bayan da aka hana zirza-zirga don gudun yada annobar.

Ana sa ran dan wasan Brazil, Emerson da na Amurka, Christian Pulisic za su koma Stamford Bridge da wuri kamar yadda Chelsea ta bukata.

Da zarar 'yan wasan sun koma Ingila za su bi dokar da gwamnati ta kafa da ta shafi killace kai da kuma bayar da tazara.

Gwamnatin Burtania za ta killace duk wanda ya shiga kasar na kwana 14 tun daga ranar Juma'a.

Wasu kungiyoyin Premier da ya hada Arsenal da West Ham da kuma Brighton sun amince 'yan wasansu su yi atisaye a matakin daidaiku da kuma bayar da tazara,

Sai dai har yanzu Chelsea ba ta bude wajen atisayenta ba da ake kira Cobham kawo yanzu.