Mauro Icardi ya kammala komawa PSG daga Inter Milan

Asalin hoton, Getty Images
Paris St-Germain ta dauki dan wasan tawagar Argentine, Mauro Icardi daga Inter Milan kan fam miliyan 54.
Dan wasan mai shekara 27, ya je PSG domin buga mata wasannin aro a watan Satumba da yarjejeniyar sayar da shi idan ya taka rawar gani.
Cikin kunshin kwantiragin da ya saka hannu a kungiyar ta Faransa, zai ci gaba da yi mata tamaula har karshen watan Yunin 2024.
Icardi ya ci kwallo 20 a wasa 31 da ya buga PSG kafin a dakatar da gasar Faransa, wadda aka kawo karshe ranar 30 ga watan Afirilu da sauran wasanni 10 saboda bullar cutar korona.
Icardi yana buga gurbi iri daya da na dan wasan Uruguay, Edison Cavani, wanda shi ne ke kan gaba a tarihin ci wa PSG kwallaye, wanda yarjejeniyarsa zai kare ranar 30 ga watan Yuni.
Hukumar da ke kula da gasar Faransa ta bai wa PSG kofin bana, bayan da kungiyar ta ja ragamar wasannin shekarar nan da tazarar maki 12 tsakaninta da ta biyu a teburi Olympique Marseille.
Wadanda suka yi kan gaba a cin kwallaye a gasar Faransa:
- Wissam Ben Yedder Monaco 18
- Kylian Mbappe Paris Saint-Germain 18
- Moussa Dembele Olympique Lyonnais 16











