Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sir Chips Keswick ya yi ritaya a matsayin shugaban Arsenal
Sir Chips Keswick ya ajiye aikin shugabantar Arsenal, bayan shekara bakwai da ya yi a kan mukamin.
Mai shekara 80 yana cikin jami'an kungiyar tun 2005 ya kuma zama shugaba a 2013, bayan da ya maye gurbin Peter Hill-Wood.
Arsenal ta ce za ta ci gaba da aiki manyan jami'anta da suka hada da Stan da Josh Kroenke da Lord Harris da kuma Ken Friar.
Keswick ya ce a karshen kakar bana ya yanke shawarar yin ritaya, sai kuma bullar cutar korona ta tsayar da komai.
Stan da Josh sun yi wa Keswick godiya da fatan alheri kan yadda ya gabatar da aikinsa, musamman daga darajar Arsenal a shekara 15 da ya yi mata aiki.
A lokacin da Kewsick ke shugabancin Arsenal, kungiyar ta ci FA Cup uku, sannan ba ta taba karkare Premier League a wajen 'yan shidan farko a gasar ba