Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal za ta hukunta Alexandre Lacazette
Arsenal ta ce ta dauki abin da dan wasanta Alexandre Lacazette da ya yi na shakar sinadarin nitrous oxide daga cikin balan-balan ba da wasa ba.
Guners ta ce za ta dauki matakan ladabtarwa da ya dace na cikin giba kan dan wasan.
Tun a baya Arsenal ta taba jan kunnen dan wasan na Faransa kan irin wannan laifin, inda aka ganshi a wani faifan bidiyo da balan-balan a bakinsa da aka ce ya tura wa wani abokinsa ne in ji wani rahoto daga jaridar Daily Star.
Shi dai wannan sinadarin na nitrous oxide da ke cikin balan-balan, idan aka shake shi yana sa bacci da rage gajiyar jiki, wasu kuma na amfani da shi wajen maye.
A cikin shekarar 2018 ne aka ja kunnen Lacazette, bayan da aka yi bidiyonsa yana shakar sinadarin a balan-balan a gidan rawa tara da 'yan wasan Gunners.
Wannan ne laifi na biyu da dan kwallon ya aikata kwanan nan, bayan da ya karya dokar bayar da tazara da gwamnati ta saka saboda gudun yada cutar korona.
Cikin watan Maris aka dakatar da dukkan wasannin Premier don kaucewa yada annobar.