Aaron Ramsdale: Golan Bournemouth ya kamu da coronavirus

An wallafa

Golan Bournemouth Aaron Ramsdale ya ce yana cikin mutum biyu da suka kamu da cutar korona bayan gwajin da hukumomin Gasar Premier suka yi masa.

A makon jiya an yi wa 'yan wasa da ma'aikata 996 gwajin cutar korona a zagaye na biyu na gwaje-gwajen da ake yi wa 'yan kwallon. Sai dai ba a fadi mutum na biyu da ya harbu da cutar ba.

An tabbatar mutum takwas da ke Gasar Premier sun kamu da korona cikin mutum 1,744 da aka yi musu gwajin cutar.

Ramsdale, mai shekara 22, wanda gwajin da aka yi masa ranar Litinin ya nuna ba ya dauke da cutar, ya shaida wa jaridar told the Sun cewa bai nuna alamar kamuwa da cutar ba.

"Wannan lamari ya yi matukar girgiza ni. Ban yi mu'amala da kowa ba amma ga shi yanzu ina dauke da cutar," a cewar dan wasan na Ingila, wanda za a killace tsawon kwana bakwai.

A gwajin da aka yi na zagayen farko an gano mutanen da dama sun kamu da cutar, ciki har da dan wasan Watford Adrian Mariappa da kuma mataimakin kocin Burnley Ian Woan.

Ana sa ran za a fitar da sakamakon gwaji zagaye na uku ranar Laraba.